Wannan littafi shine littafi na farko a cikin jerin littattafai gida uku da Alhaji Abubakar imam ya rubuta a wata shida na zamansa a zariya a shekarar 1936. Ya kunshi labarai masu kayatarwa, fadakarwa da ban dariya. Labaran Har guda ashirin da tara, zasu natsar da mai karatun su, sannan su rike hankalin sa Har Sai sun Zame masa abun kauna.